Om Bisharan Markus
Lokacin da mu ke fuskantan damuwoyi da wahala a duniya, mu na bukatan karfafawa. Lokacin da ba mu san inda za mu sa kan mu ba, mu na bukatan bege. Lokacin da mu ka yi zunubi, mu na bukatan Mai Ceto. Lokacin da mu ke shakka bangaskiyan mu, mu na bukatan tabbaci.
Yesu ne karafawan mu, begen mu, Mai Ceton mu da kuma tabbacin mu. Shi ne Mai Ceton da mun yi ta jira, wanda duk cikin tarihi a ke jira. Shi ne ¿an Allah. Shi ne Kristi.
"Hakika mutumin nan ¿an Allah ne!" -Mark 15:39
Bisharan Markus labarin rayuwan Yesu ne mai iko sosai. Ya nuna halin Yesu a kowani shafi, daga so Ya sha wahala kuma Ya yi hidima zuwa ga nuna ikon Shi da Allantakan Shi. A kowani labari sai marubucin na tambaya, "Ina bangaskiyan ki?" Yayinda mu ku karanta da kuma binciken Markus, dole mu tambaye kan mu ko bangaskiyan mu na cikin Yesu ko cikin kan mu.
Bisharan Markus binciken Littafi mai Tsarki ne a kan Bisharan Markus. Yayinda za mu ¿auki makonni shida mu na biniciken wannan labarin rayuwan Yesu mai muhimmanci, bari mu tambay ikan mu tambayan da ya fi muhimmanci: "Ina bangaskiyan ki?" - Akwai bayyanai biyu wanda su ka fi karfi akan wanene Yesu a duk cikin wannan Bisharan. Yayinda mu ke duba wannan littafin tare, mu na begen za mu iya amsa tambayan wanene Yesu Kaman yadda Bitrus ya yi: "Kai ne Almasihu" (Mk 8:29). Idan kin a so ki samu bangaskiya mai karfi akan wanene Yesu da kuma abin da Zai iya yi, wannan ne binciken Littafi mai Tsarki domin ki!
Mu häa kai a yannan gizo domin wannan bincike na tsawon mako shida ko kan app namu na Love God Greatly. -A can za ki samu abubuwan da ya shafi Bisharan Markus a duka wurare biyu tare da rubuce rubucen mu na Littinin, Laraba da Jumma'a, da Karin bayyani ta wurin karatun mu na kullum, da kuma jama'a masu kauna domin su karfafa ki yayinda ki ke so ki kara koyi kan Mai Ceton mu kuma mu girma ciken bangaskiyan mu a cikin Shi.
Visa mer